Manhajoji da aka Nuna
Sami ƙari daga OneNote tare da waɗannan manhajoji da kuma na'urori.
Brother Web Connection
Brother machine ɗinka (MFP/Sikanar Daftarai) zai iya sikanin hotuna da kuma loda su zuwa OneNote da kuma OneDrive kai tsaye ba tare da zuwa wata kwamfuta ba.
Chegg
Dalibai suna iya adana tsannanin amsoshin aikin gida ɗinsu daga Chegg Study Q&A zuwa OneNote. Yana da sauƙi da maɓallin “Kafa Shi” na OneNote. Daga can, kana iya fara tsarawa amsoshinka ta batu, aji ko aikin gida kuma ka samu neman dukan su nan take a cikin OneNote. Ƙirƙiri babban ja-goran karatu sai kuma a raba tare da abokan ajinka.
cloudHQ
Haɗe bayananka na OneNote tare da cloudHQ. Daidaita littattafan rubutunka tare da fitattun sabis-sabis na gajimare kamar Salesforce, Evernote, Dropbox. Yi haɗin gwiwa tare da wasu cikin sauƙi, raba tuninka a cikin duk wata manhaja, da kuma daidaita su kai tsaye zuwa OneNote. Haka nan yi wa littattafan rubutunka wararriyar ajiya cikin sauran sabis-sabis na gajimare don kare tunaninka idan ka share su bisa kuskure.
Newton
Adana muhimman imel-imel zuwa OneNote da kawai wani danne ta yin amfani da Newton. Ko wata takardar farashi ne, wani bayanin girki, ko imel na wani muhimmin abokin ciniki, yi amfani da Haɗuwar OneNote na Newton don riƙe komai tare.
Docs.com
Docs.com yana bari masu amfani su yaɗa rubuce-rubuce ko kayan aikin koyo ta littattafan OneNote. Yana ba wa mutane kamar malamai da ɗalibai a dukan duniya damar dubawa da kuma sake yi amfani da littafin rubutu na OneNote, wanda yake ƙara tashe da tasiri a cikin al'umma.
Doxie Mobile Scanners
Doxie wata sabuwar sikana ce ta takarda da ake iya cajinta, saboda haka za ka iya sikanin daftarai a ko'ina - ba a buƙatar kwamfuta. Kawai ka yi cajinta ka kuma kunna ta, a duk inda kake - saka takardarka, rasiɗai, da kuma hotuna don sikanin, ajiyar tarihi. Doxie yana sikanin a ko'ina, sannan ka daidaita zuwa OneNote don iso ga duk daftaranka da ka yi sikanin, a kan duk na'urorinka.
EDUonGo
EDUonGo yana ƙyale kowa ya ƙaddamar da makaranta ko kwas na kan layi a cikin mintoci. Ɗaliban EDUonGo za su iya fitar da darussa cikin sauƙi zuwa littattafan rubutunsu na kansu. Haka nan ɗalibai za su iya haɗi zuwa asusu-asusun OneDrive ɗinsu. Ga malamai kuwa, za su iya haɗawa da bidiyoyi daga Office Mix a cikin darussanku.
Imel zuwa OneNote
Ɗauki abubuwan da suke da muhimmanci gare ka a yayin da kake tafiya ta aika su ta imel kai tsaye zuwa littafin rubutunka! Aika daftarai, bayanai, tsare-tsaren tafiya, da kuma ƙari da dama zuwa me@onenote.com kuma za mu iya sa su a cikin littafin OneNote ɗinka, a inda za ka iya samun iso gare su daga duk na'urorinka.
Epson Document Capture Pro
Document Capture Pro yana ba ka damar sikanin daftarai cikin sauƙi, gyara shafuka, adana fayiloli da kuma tura bayanai zuwa manhajoji da aka yi sakanin tare da sikanoni na Epson kamar Workforce® DS-30, DS-510, DS-560 da sauransu. Mene ne ƙari, masu amfani za su iya sika zuwa OneNote tare da taɓawa ɗaya, don samun iso cikin sauƙi ga datarai daga ninkin na'urori ko rabawa tare da saura.
eQuil Smartpen2 & Smartmarker
Yi rubutu a kan duk wani wuri ka kuma aika su zuwa OneNote ta mayar da shi wuri mai dabara tare da eQuil Smartpen2 da kuma Smartmarker. Hanya ce ta ɗaukar abubuwa masu ban sha'awa.
Feedly
Feedly yana haɗa masu karatu tare da labarai da kuma bayanai da suke da sha'awa a kai. Yi amfani da feedly don gano da kuma bin babbar ƙunshiya, sannan ka adana maƙaloli mafi kyau kai tsaye zuwa OneNote tare da taɓawa ɗaya.
Paper da Pencil ta wajen FiftyThree
Tafi daga Pencil zuwa Paper da dabarunka sa’an nan kuma ɗauki wani mataki a gaba da OneNote. Yi rubutu kuma zana da bunƙasasshen daidaitywa da sauƙi da aka san Pencil da shi, kuma idan ka yi wani kuskure kawai juya alƙalamin waya ɗin kuma share da ainihin hanya -duka kai tsaye a cikin OneNote. Ɗauki bayanai da sauƙi, yi jerin buƙatun aiki kuma yi zane a cikin Paper sa’an nan raba zuwa OneNote don a yi ƙari, kamar yi aiki tare a cikin wani rababben littafin rubutu, ƙara naɗe-naɗen sauti ciki kuma iso ga ƙunshiyarka daga kusan kowace na'ura.
Genius Scan
Genius Scan wata sikana ce a cikin aljihunka. Tana ba ka damar mayar da daftaran takarda zuwa dijital, ƙirƙirar fayilolin PDF tare da adana su nan-da-nan a cikin OneNote.
JotNot Scanner
JotNot yana mayar da iPhone ɗinka zuwa wata sikana mai ninkin shafi. Za ka iya amfani da JotNot don sikanin daftarai, rasiɗai, fararen allo, katinan kasuwanci da kuma rubutu a cikin wani tsari na lantarki. JotNot yanzu yana samar da haɗewar kai tsaye tare da dandalin OneNote na Microsoft, saboda ka iya adani cikin sauri da kuma sauƙi da kuma shirya sikan ɗinka ta amfani da asusunka na OneNote.
Livescribe 3 Smartpen
Tare da Livescribe 3 smartpen da kuma manhajar Livescribe+, kawai ka yi rubutu a kan takarda ka kuma ga komai yana bayyana nan-take a kan na'urarka ta wayar hannu, inda za ka iya sa alama, nema da kuma juya bayananka zuwa rubutu. Za ka iya aika komai zuwa OneNote saboda haka ana haɗe rubutunka na hannu da kuma zane-zane tare da sauran muhimman bayananka.
Mod Notebooks
Mod wani littafin rubutu ne na takarda da ake samun iso gare shi daga gajimare. Ɗauki rubutu da wani alƙalami ko takarda da ka san ta, sannan ka mayar da shafukanka dijital a kyauta. Kowane shafi na wani littafin aiki da aka kammala za a iya daidaita shi da OneNote a kuma adana shi har abada.
NeatConnect
NeatConnect yana juta fayilolin takarda zuwa daftaran dijital ya kuma aika su kai tsaye zuwa OneNote - ba tare da wata kwamfuta ba. Daga kowane ɗaki a cikin gidanka, ko daga kowane wuri a cikin ofishin, jituwa na Wi-Fi ɗin NeatConnect da kuma allon taɓawa yana sa sikanin zuwa OneNote sauri da kuma gajarce lokaci, ya mayar da tsarawa da samarwa zuwa wasu sababbin matakai.
News360
News360 wani keɓaɓɓen manhajar labarai ne da yake sanin abin da kake so da kuma ƙwarewa a yayin da kake amfani da shi. Tare da sama tushe fiye da 100,000, a koyaushe akwai abubuwan karantawa, kuma za ka iya adana labaranka mafiso kai tsaye zuwa OneNote tare da taɓa wani maɓall.
Nextgen Reader
Wani makarancin RSS mai sauri, mai tsabta kuma mai kyau don Windows Phone. Yanzu yana bari ka adana maƙaloli kai tsaye a OneNote. A ji daɗi karatu!
Office Lens
Office Lens kamar samun wata sikana ce a cikin aljihunka. Kada ka sake rasa rubutu a kan wani farin allo ko baƙin allo, kuma kada ka taɓa neman daftarai da aka manta inda aka ajiye su ko katin kasuwanci, rasa rasiɗai ko rubutu na mannawa! Office Lens yana sa sake sa hotunanka sake-amfani. Ɗauki ƙunshiya kai tsaye a cikin OneNote tare da yankewa ko gyarawa na otomatik.
OneNote For AutoCAD
OneNote don AutoCAD zai bari ka ɗauki rubuce-rubuce tare da zanenka daga cikin AutoCAD. Wannan yana ƙara ƙwazon aiki na gwanayen zanen gini da ilimin aikin injiniya a dukan duniya ta yin amfani da AutoCAD don ƙirƙira zane-zanen 2D da 3D. Ana yi tsimi waɗannan rubuce-rubuce zuwa taron hanyoyin sadarwa kuma ana iya iso ga su a kowane lokaci. Masu amfani suna iya gani waɗannan rubuce-rubuce a lokaci na gaba da suke buɗe zanen a cikin AutoCAD.
OneNote Class Notebooks
Tsara shirye-shiryen darasi da ƙunshiyar kwas ɗinka a cikin littafin rubutu na dijital na kanka ta yin amfani da wani keɓaɓɓen fagen aikin kwamfuta don kowane ɗalibi, wani laburaren ƙunshiya don maƙaloli, da kuma wani sararin haɗin kai don darusa da ayyuka masu fasaha.
OneNote Web Clipper
OneNote Web Clipper yana ba ka damar adana shafukan yanar gizo daga burauzarka a cikin littattafan rubutun OneNote ɗinka. Cikin dannawa ɗaya kawai, yana taimaka maka ɗaukar abubuwa cikin sauri da kuma tunar da ƙari a cikin rayuwarka.
Powerbot for Gmail
Adana imel masu muhimmanci, tattaunawa da maƙalawa a OneNote kai tsaye daga fuskar hulɗa na Gmail. Babu tsallakewa nan da can tsakanin ƙa’idodi kuma.
WordPress
Rubuta bugawarka ta WordPress a kan kowace na'ura, a kan naúrori mabambanta, kan layi ko wajen layi a kan OneNote da kuma sauƙin sake amfani daga duk bayananka da suke akwai.
Zapier
Zapier ita ce hanya mafi sauƙi wajen haɗi da OneNote tare da manhajojin da ka riga ka yi amfani da su, kamar Salesforce, Trello, Basecamp, Wufoo da kuma Twitter. Yi amfani da wannan manhaja don adana bayanai, ajiye bayanin ɗawainiyoyi da aka adana ko adana sababbin abokan ma'amala, hotuna, shafukan yanar gizo da kuma ƙari.